logo

HAUSA

Kungiyoyin mata na nuna damuwa kan yadda matasa suke ta’ammali da kayan maye a cikin makarantun birnin Yamai

2023-02-24 11:27:49 CMG Hausa

Matasa a birnin Yamai na ta’ammali da kayan maye, matsalar dake tada hankalin iyaye mata, ganin yadda matsalar take kokarin mamaye makarantun firamare da na sakandare na babban birnin, inda wasu makarantun za ka tarar da ’yan makarantar suna busa tabar wiwi ko kuma daukar diyan hadiya ko kwayoyi. Domin tunkarar wannan matsalar ce kungiyar “La Voix d’une Mère” cewa da kungiyar Muryar ma’aifiya ta fara aikin wayar da kan dalibai da ’yan makaranta, domin gargadinsu da su kiyaye kansu da miyagun kwayoyi.

Daga jamhuriyar Nijar wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da rahoto.

Dalilin ke nan, na fara tambayar madam Gueye Fatouma Laouali, shugabar kungiyar “la voix d’une mère”, wato muryar ma’aifiya, ko yaya take dubin wannan matsalar ?

Wallahi matsala ce babba, saboda a bangaren matasa babu inda za ka shiga, lungu-lungu a cikin Yamai babu wannan tashin hankali. E idan ka shiga kan titi, yara ne wadanda ba su zuwa makarantar boko ne, har ma da masu makarantar allo cewa da almajirai, Subbahanallahi suna cikin wannan halin ne, ke nan a ko ina ne aka samun wannan matsala, kuma abin da ke da ciwo abin bai ja da baya kullum sai ci gaba yake yi. Ke nan ya kamata mu zauna ga baki daya, tun da matsalar tuni mun gano ta, akwai ta, ke nan kamata ya yi mu zauna ga baki dayanmu. Mu iyaye da muka aifi yaran nan, da gwamnati da take da nauyin al’umma gaba daya a kanta da malamai da duk wadanda abin ya shafa, saboda wannan abin ya shafi al’umma gaba daya, mu zauna mu hada kanmu, mu samu mafita a kan wannan al’amarin.

To sai dai kuma, shugabar kungiyar muryar ma’aifiya, dole sai kowa ya san nasa laifi, inda ta kara da cewa,

Laifi da farko iyaye ne, e a yau mu ne, ai shi ya sa muka fito, mun yi la’akari da mu ne muka kasa, kuma tarbiyar yara, uwaye biyu suke yin ta, amma uwa nauyin yana bisa kanta, saboda uba, yana da charge da yawa wato yana da nauyi da yawa, zai tashi da darurar mi zai kawo muku ku ci, ke nan ko da yaron yana wani abu hankalinsa bai kawo ba ma, amma kuma ke uwa, ya kamata, kuma idan ta bace ke kuma kike fara kuka, ke nan ki ma kanki maganin abin da za ki mishi kuka. Ke nan mu mun yarda da cewa mu muka bata, kuma mu ne mu kamata mu tashi mu gyara.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijar.