logo

HAUSA

AU ta ce a shirye take ta dafawa Najeriya wajen girka ingantacciyar demokradiyya

2023-02-23 19:23:53 CRI

 

A ranar Laraba 22 ga wata, masu sanya ido kan zaben Najeriya daga kungiyar tarayyar Afrika suka kara tabbatar da aniyar kungiyar na ganin cewa Najeriya ta kai ga samun nasarar zabukan dake gaban ta wanda za a fara daga ranar Asabar 25 ga wata.

Shugaban ayarin kungiyar AU da za su saka idanun kan zaben na Najeriya, tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ne ya tabbatar da hakan a birnin Abuja lokacin da ya jagoranci wakilan kungiyar zuwa wajen ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama.

Daga tarayyar Najeriya wakili mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.