logo

HAUSA

Hukumar zaben Nijeriya ta fara rarraba kayan zabe a cikin kasar

2023-02-23 13:42:30 CMG Hausa

Hukumar zaben mai zaman kanta a Najeriya wato INEC, ta fara rabon kayan zabe a fadin kasar, gabanin zaben shugaban kasar da za a yi a karshen mako. Kayayyakin da aka rarraba sun hada da takardun zabe na musamman, da wadanda ake rubuta sakamako da kuma injunan tantance masu zabe (BVAS).

Haka kuma, a wani yunkuri na tabbatar da sahihancin zabukan dake tafe, hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, a ranar Larabar da ta gabata ta ce ta tura jami’anta domin yaki da saye da sayar da kuri’u a fadin Najeriya

Kungiyar tarayyar Afirka AU ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Talata cewa, tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya isa birnin Abuja na Najeriya, domin jagorantar tawagar AU mai sanya ido kan zaben na Najeriya mai mambobi 90 a kasar, wadanda za su sa ido don ganin an gudanar ingantaccen zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin Najeriya da aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabrairu. (Safiyah Ma)