logo

HAUSA

Rukunin ma’aikatan lafiya na sojojin kiyaye zaman lafiya da Sin ta tura zuwa Mali ya ci jarrabawar binciken na’urorinsa

2023-02-23 14:05:56 CMG Hausa

Rukunin ma’aikatan lafiya na 10 na sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura zuwa Mali, ya ci jarrabawar binciken na’urorinsa da MDD ta gudanar a farkon watanni uku na wannan shekara. A yayin da aka gudanar da jarrabawar, rukunin ma’aikatan lafiya sun adana nau’o’in na’urorinsu yadda ya kamata, na’urorin da kuma suka yi aiki yadda ya kamata, kuma hakan ya samu yabo daga tawagar binciken.

MDD na gudanar da bincike a kan na’urorin jami’an kiyaye zaman lafiya da kasa da kasa suka tura don tabbatar da ayyukan kiyaye zaman lafiya sun gudana yadda ya kamata. (Lubabatu)