Wajibi ne a gudanar da bincike na gaskiya game da lamarin bututun “Nord Stream”
2023-02-23 21:32:53 CMG Hausa
Bisa bukatar kasar Rasha, kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da wata muhawara a bainar jama’a kan fashewar bututun iskar gas na “Nord Stream”. inda mambobin kwamitin suka bayyana matsayinsu. Kasar Sin ta bayyana karara cewa, gudanar da bincike na hakika, rashin son kai, da kwararru kan lamarin, yana da alaka da moriya da damuwar kowace kasa, kuma tana goyon bayan hanzarta aiwatar da bincike da gano gaskiya nan da nan.
Da farko dai, bututun “Nord Stream” wani muhimmin ababen more rayuwa ne na kasa da kasa, kana cibiyar sufurin makamashi. Lalata ta, ta yi mummunar tasiri ga kasuwannin makamashi na duniya da muhallin halittu. Al’ummar duniya suna da 'yancin sanin gaskiya, kuma kada su bari ta hakan ya tafi a banza. Sannan a kalli yanayin muhalli. Fashewar bututun, ta haifar da yoyon miliyoyin cubik na iskar. Bugu da kari, lamarin har yanzu batu ne na siyasa, wanda ya shafi tsaro da zaman lafiyar kasashen Turai baki daya. Abu mafi mahimmanci, idan aka fuskanci cikakkun bayanai na zahiri da karin shakku, wajibi ne a gudanar da bincike na hakika da rashin son kai game da lamarin, don kara tabbatar da gaskiya da adalci a duniya. (Mai fassarawa: Ibrahim)