Kasar Sin za ta fito da sabbin matakai kan aikin nazari daga tushe
2023-02-23 13:49:55 CMG Hausa
Ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis mai mulki ta kasar Sin ya gudanar da taron kara wa juna sani a ranar 21 ga wata. Babban sakataren kwamitin kolin Mr. Xi Jinping ya jagoranci taron, inda ya jaddada cewa, ya zama dole a karfafa aikin nazari daga tushe a wani kokari na tabbatar da dogaro da kai ta fannin kimiyya da fasaha, da kuma raya kasa mai karfin kimiyya da fasaha. Ya ce, kamata ya yi sassan jam’iyyar da ma hukumomi na matakai daban daban su sanya aikin cikin ajandarsu, su kara karfin tallafa wa aikin ta fannin fito da manufofi, don inganta aiki yadda ya kamata. Xi Jinping ya kuma jaddada cewa, ya kamata a kafa dandalin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa ta fannin yin nazari daga tushe, da kafa asusun nazari da zai kunshi kasashen duniya, kuma a fadada hadin gwiwar Sin da kasashen ketare a fannonin nazarin sauyin yanayi da tsaron makamashi da halittu da ma bunkasa harkokin sararin samaniya.
Me ya sa aka dora muhimmanci kan aikin nazari daga tushe? Saboda in babu aikin nazari daga tushe, to ba za a samu ci gaban kimiyya da fasaha ba. Haka kuma, yanzu kasar Amurka ta mayar da kasar Sin babbar abokiyar takararta, tana yunkurin dakile ci gaban kasar Sin da hadin gwiwar kawayenta. Ta kuma ci zalin kasar Sin ta fannin kimiyya da fasaha na zamani. Don haka ya zama tilas kasar Sin ta gaggauta inganta aikin nazari daga tushe, don ganin an warware wasu matsaloli daga tushe. (Tasallah Yuan)