logo

HAUSA

Sin na ci gaba da aiwatar da shawarwari masu inganci daga tarukan NPC da CPPCC

2023-02-23 19:31:08 CMG Hausa

A jiya Laraba ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya saurari rahoton yadda ake tafiyar da shawarwarin da wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC, da mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC suka gabatar cikin shekarun da suka gabata.

Wata sanarwa da aka fitar bayan taron ta bayyana cewa, yayin da yake jagorantar taron zartaswar majalisar gudanarwar kasar ta Sin, Li ya kuma shirya gudanar da ayyuka kan sauraron shawarwari daga wakilan NPC da na CPPCC a yayin zaman taruka biyu na bana.

A bara ne, ofisoshi da sassan da ke karkashin majalisar gudanarwar kasar, suka gabatar da shawarwari 8,721 daga wakilai NPC, da kuma shawarwari 5,865 da mambobin kwamitin CPPCC suka gabatar. (Ibrahim)