logo

HAUSA

Xi Jinping ya ba da umurnin koyon ruhin Lei Feng

2023-02-23 20:13:19 CMG HAUSA

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurni a kwanan baya cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 60 da wasu manyan shugabannin kasar ciki hadda Mao Zedong suka rubuta kalmomin yabawa jarumi Lei Feng , kuma ana ci gaba da zurfafa ayyukan koyon ruhin Lei Feng, wato taimakawa. Abin da ya nuna cewa, wannan ruhi ba zai canja ba duk da canjawar lokuta.

Xi Jinping ya nanata cewa, kamata ya yi a nace ga ruhin Lei Feng don taimakawa jama’a da ba su jagoranci, da habaka wannan aiki cikin al’umma, ta yadda matasa za su taka rawarsu wajen zamanintar da mulkin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin, da ingiza farfadowar al’ummar Sinawa daga dukkan fannoni.(Amina Xu)