Zaunannen kwamitin majalisar wakilan kasar Sin ya fara zamansa
2023-02-23 19:15:56 CMG Hausa
A yau Alhamis ne, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, ya fara zama na 39 a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Li Zhanshu, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC), shi ne ya jagoranci babban taron farko na zaman. (Ibrahim)