Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta lashe kofin ‘Club World Cup’ karo na biyar bayan doke Al Hilal da ci 5-3.
2023-02-22 15:33:30 CRI
Jerin ‘Yan Wasan Da Kwantiranginsu Zai Kare A Karshen Kakar Bana
A karshen watan janairun wannan shekarar ta 2023 aka rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a wasu kasashen Turai, sai kuma karshen kakar nan za a ci gaba da hada-hadar kaka ta gaba.
To sai dai kuma kamar yadda doka ta tanada kungiyoyi za su iya sayen wadanda kwantiraginsu zai kare zuwa karshen kakar nan wanda hakan yake nufin kungiya za ta dauki wanda yarjeniyarsa ta kusan karewa zuwa karshen kakar nan da wanda ba shi da wata kungiyar da yake da yarjejeniya da ita.
Cikin ‘yan wasa da ke kasa a yanzu akwai Isco, shi ne wanda ke da kwarewa da yawa, bayan lashe kofuna da yawa a kungiyar Real Madrid dan kwallon tawagar Sifaniya ya lashe kofin zakarun turai na Champions League guda biyar da Club World Cup guda hudu da La Liga uku da Uefa Super Cup uku da Copa del Rey.
A cikin watan Disamba dan wasan da Sevilla suka amince kowa ya kama gabansa, an kuma sa ran a karshen Janairu zai koma kungiyar kwallon kafa ta Union Berlin daga baya batun ya bi ruwa yayin da wakilinsa ya yi wa Manchester United tayin dan wasan bayan jin ciwon Cristian Eriksen.
Jerin wasu ‘yan wasan da za a iya dauka a wannan lokacin
Sime Brsaljko dan kasar Croatia, mai tsaron baya, mai shekara 31 da Jese Rodriguez dan kasar Spain, mai tsaron baya, mai shekara 29 da Federico Fernandez dan kasar Argentina, mai tsaron baya, mai shekara 33.Akwai kuma Jordan Lukaku dan kasar Belgium, mai tsaron baya, mai shekara 28 da Bojan Krkic dan kasar Spain, mai cin kwallaye, mai shekara 32 sannan akwai Jurgen Locadia dan kasar Netherlands, mai cin kwallaye, mai shekara 29 sai Renzo Sarabia dan kasar Argentina, mai tsaron baya, mai shekara 29 da Pape Cheikh Diop dan kasar Senegal, mai wasa daga tsakiya, mai shekara 25.
Gakpo Ya Yi Gaggawar Koma Wa Liverpool, Cewar Koeman
Kociyan tawagar kasar Netherlands, Ronald Koeman ya ce Cody Gakpo ya yi saurin koma wa Liverpool bayan ya kasa taka rawa a kungiyar da ke fuskantar kalubale a bana.
Mai shekara 23 ya taka rawar gani a gasar kofin duniya a Katar da cin kwallo uku a wasa biyar, bayan da Netherlands ta kai wasan kusa dana kusa dana karshe a gasar da Argentina ta yi waje da su.
Sai dai ya kasa cin kwallo a wasanni shida a Liverpool, tun bayan da ya koma daga PSB Eindhoben a watan Janairu bayan da farko kungiyar Manchester United ta yi zawarcinsa.
Koeman ya ce ”Ya koma kungiyar da ba ta yin kokari a kakar nan kuma abu ne mai dan karen wahala a makomar dan wasa matashi da baya cin kwallo, kuma kungiya ba ta cin wasanni, sannan ba a ganin mahimmanci ka.”
Ya kara da cewa ”Idan dan wasa ne da ya kai shekara 28 mai dinbin kwarewa, abin zai zama na daban.”
Koeman tsohon kociyan Everton, wanda ke jan ragamar Netherlands karo na biyu ya ce matashin dan wasan Netherlands kan fuskanci kalubale idan ya koma fitatciyar kungiya.
Kafin Gakpo ya koma Liverpool ya ci kwallo tara ya bayar da 12 aka zura a raga a wasa 14 a PSB a kakar bana a babbar gasar kasar Netherlands sai dai Liverpool, wadda aka fitar da ita daga Carabao da FA Cup a bana tana ta 10 a teburin Premier League da maki 29, za ta kara da Real Madrid a Champions League.
Liverpool ta yi rashin nasara da ci 3-0 a hannun Wolberhampton a wasan mako na 22 a gasar Premier League a satin daya gabata kuma da wannan sakamakon Liverpool , wadda ta yi wasa 20 tana ta 10 a teburin firimiyar Ingila da maki 29.
Wasa na bakwai kenan da Liverpool ta kara a shekara 2023, kuma daya daga ciki tayi nasara shi ne a FA Cup da ta doke Wolbes 1-0 to sai dai har yanzu Liverpool ba ta karawa ba a gasar Premier a 2023 a wasa hudun da ta fafata kawo yanzu.
Jerin wasannin da Liverpool ta buga a 2023:
Premier League Litinin 2 ga watan Janairu Brentford 3 – 1 Liverpool FA CUP Asabar 7 ga watan Janairu Liverpool 2 – 2 Wolbes Premier League Sa 14 ga Jan 2023 Brighton 3 – 0 Liverpool
FA CUP Talata 17 ga watan Janairu Wolbes 0 – 1 Liverpool Premier League Asabar 21 ga watan Janairu Liverpool 0 – 0 Chelsea FA CUP Lahadi 29 ga watan Janairu Brighton 2 – 1 Liverpool Premier League Asabar 4 ga watan Janairu Wolves 3 – 0 Liverpool Wasa uku na gaba da Liverpool za ta buga Premier League Litinin 13 ga watan Fabrairu Liverpool da Everton Premier League Asabar 18 ga watan Fabrairu Newcastle da Liverpool Champions League Talata 21 ga watan Fabrairu. Liverpool da Real Madrid.
Real Madrid Ta Lashe Kofin ‘Club World Cup’ Karo Na 5
Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta lashe kofin ‘Club World Cup’ karo na biyar bayan doke Al Hilal da ci 5-3.
Madrid da doke Al Hilal ne a daren ranar Asabar da ya gabata a Kasar Maroko.
Vinicius Junior da Fede Velverde ne suka zura wa Real Madrid kwallo biyu kowanensu, sai Benzema da ci kwallo daya.
Ita kuwa Al Hilal Musa Marega ya ci kwallo daya sai Louis Vietto da ya ci mata kwallo biyu.
Wannan dai shi ne karo na biyar da Real Madrid ke lashe wannan kofi a tarihinta.
Wannan kofi da ta dauka ya kawo adadin kofi 100 da kungiyar ta dauka tun bayan kafuwarta.