logo

HAUSA

Algeriya ta tuso keyar mutane 2298 zuwa garin Assamaka na kasar Nijar

2023-02-22 09:31:21 CMG Hausa

A kwanan baya, kasar Algeriya ta tuso keyar mutane 2298 zuwa garin Assamaka na kasar Nijar. Yanzu ga rahoton da wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana daga Jamhuriyar Nijar.

Ayarin motoci uku ne shake de mutane aka tuso keyarsu daga Aljeriya zuwa garin Assamaka na kasar Nijar mai iyaka da Algeriya a ranakun 10, da 12 da 14 ga watan Fabrairun shekarar 2023, a cewar wata kungiyar agaji da rajin kare hakkin dan adam ta Sahara, lamarin da hukumomin wurin suka tabbatar. A cewar kungiyar, Assamaka na fuskantar matsalar jin kai mai tsanani dalilin zuwan wadannan mutane da aka kora daga Aljeriya, tuni dai kungiyar kula da ’yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya cewa da OIM ke ci gaba da kokarin tafiyar da ayyukan kula da kwararar wadannan sabbin ’yan gudun hijira. A cewar masu rajin kare hakkin dan adam na kungiyar Phone Sahara da ke Assamaka, kafin zuwan wannan ayarin motocin, akwai wasu 1000, da suka rasa matsugunni a Assamaka. Hakan ya sa, kungiyoyin jin kai da kare hakkin dan adam suka fara kiraye-kiraye, kan halin da miliyoyin ’yan gudun hijira dake Nijar za su shiga, idan ba a gaggauta daukar matakan da suka dace ba, wadannan mutane za su kara shiga cikin yanayi mai tsanani, inda suka kara bayyana cewa yawancin wadannan mutane da aka kora daga kasar Aljeriya sun rasa samun ayyukan kungiyar kula da ’yan gudun hijira ta MDD yadda ya kamata.

A cewar alkaluman baya bayan nan na kungiyar agaji da rajin kare hakkin dan adam ta “ les lanceurs d’alerte d’Alarme Phone Sahara ” da ke Assamaka, a kalla mutane 24,250 Aljeriya ta kora zuwa Nijar a shekarar 2022.

Yayin da a farkon shekarar 2023, mutane kusan 4395, kasar Aljeriya ta kora zuwa Nijar.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyyar Nigar.