logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmancin karfafa aikin nazari

2023-02-22 14:18:51 CMG Hausa

Ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis mai mulki ta kasar Sin ya gudanar da taron kara wa juna sani karo na uku jiya da yamma. Babban sakataren kwamitin kolin Mr. Xi Jinping ya jagoranci taron, inda ya jaddada cewa, ya zama dole a karfafa aikin nazari daga tushe a wani kokari na tabbatar da dogaro da kai ta fannin kimiyya da fasaha, da kuma raya kasa mai karfin kimiyya da fasaha. Ya ce, kamata ya yi sassan jam’iyyar da ma hukumomi na matakai daban daban su sanya aikin cikin ajandarsu, su kara karfin tallafa wa aikin ta fannin fito da manufofi, don inganta aiki yadda ya kamata.

Xi Jinping ya kuma jaddada cewa, ya kamata a kafa dandalin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa ta fannin yin nazari daga tushe, da kafa asusun nazari da zai kunshi kasashen duniya, kuma a fadada hadin gwiwar Sin da kasashen ketare ta fannonin nazarin sauyin yanayi da tsaron makamashi da halittu da ma bunkasa harkokin sararin samaniya. (Lubabatu)