logo

HAUSA

Kasar Sin ta samar da dabararta don kara kiyaye tsaron duniya

2023-02-22 14:10:57 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Sin a jiya Talata ta fitar da takardar da ke bayani a kan shawarar kiyaye tsaron kasa da kasa, inda ta yi karin haske game da ainihin ma’anar abubuwan da ke kunshe a cikin shawarar, tare da fitar da wasu muhimman fannoni 20 da kasa da kasa suke iya hadin gwiwa a kai, inda kuma aka tsara taswira game da yadda za a aiwatar da shawarar.

A watan Yunin shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar kiyaye tsaron kasa da kasa, inda ya nuna wata sabuwar hanyar da ya kamata kasa da kasa su bi, wato su yi shawarwari da juna a maimakon yin fito-na-fito, kuma su yi hadin gwiwa da juna a maimakon su kulla kawance, su kuma cimma moriyar juna a maimakon cin nasara daga faduwar wani bangare. Shawarar da kawo yanzu ta samu yabo da goyon baya daga kasashe da shiyyoyi sama da 80.

Shawarar ta kuma jaddada wasu fannoni shida da ya kamata a tsaya a kai, ciki har da “martaba mulkin kai da cikakkun yankunan kasa na kasashe daban daban” da “bin ka’idojin tsarin dokokin MDD” da “dora muhimmanci a kan matsalolin tsaro da ke jawo hankalin kasa da kasa” da “daidaita rikici da arangama a tsakanin kasa da kasa ta hanyar yin shawarwari” da makamantansu.

Hakkin kasa da kasa ne su tabbatar da tsaronsu, a maimakon zama hakkin musamman na wasu kasashe kalilan. Don tabbatar da tsaron duniya, kamata ya yi kasa da kasa su dauki nauyin da ke wuyansu. Kasar Sin na fatan ganin bangarori daban daban su amince da shawarar kiyaye tsaron kasa da kasa, tare da cimma burikan dake ciki, a wani kokari na kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya. (Lubabatu)