logo

HAUSA

Xi ya ba da muhimmin umarni sakamakon rugujewar mahakar ma'adinin kwal a Mongoliya ta gida

2023-02-22 20:21:34 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da muhimmin umarni, biyo bayan rugujewar wata mahakar ma'adanin kwal a Mongoliya ta gida, inda ya bukaci da a yi duk mai yiwuwa wajen ganowa tare da ceto wadanda suka bace, da kula da wadanda suka jikkata, da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

A yau ne da misalin karfe 1 na rana, aka samu wani gagarumin rugujewar wata mahakar ma'adanin kwal a yankin Alxa dake Mongoliya ta gida, kuma ya zuwa yanzu, hadarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2, tare da jikkata mutane 6, yayin da mutane 53 suka bace. (Ibrahim)