logo

HAUSA

Masu sanya ido na gida da na kasashen waje dubu 146,913 ne hukumar INEC a Najeriya ta tantance

2023-02-22 09:25:58 CMG Hausa

A ranar Talata 21 ga wata, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya Farfessa Mahmud Yakubu ya sanar da cewa hukumar ta kammala tantance masu sanya ido kan zaben kasar  har su dubu 146,913.

A lokacin da yake ganawa da masu sanya idon a birnin Abuja, shugaban hukumar zaben ya ce wannan adadi ya kunshi masu sanya ido ’yan kasa da wadanda suka zo daga kasashen wajen.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Wannan dai shi ne karo na bakwai cikin jamhuriyya ta 4 da za a gudanar da zabe karkashin tsarin demokuradiyya a Najeriya.

A jawabinsa, farfesa Mahmud Yakubu ya ce bisa tsarin da ake gudanarwa a duniya, hukumomin zabe kan baiwa kungiyoyin kasashen duniya da kuma na cikin gida damar sanya ido kan harkokin zabe tare kuma da ba su damar shirya tarukan wayar da kai ga jami’an hukumomin zaben.

Ya ce hukumomin zaben sau tari suna karuwa sosai daga irin shawarwarin da irin wadannan kungiyoyi kan bayar kan yadda za a inganta tsare-tsaren zabuka.

Shugaban hukumar zaben ta tarayyar Najeriya ya alakanta ci gaban da tsarin demokuradiyyar kasar ta samu tun daga shekarar 1999 kan irin rahotannin da ake samu daga kungiyoyin sanya ido.

Farfessa Mahmud Yakubu ya ci gaba da bayanin cewa hukumar zaben ta samu tantance kungiyoyi na cikin gida guda 196 yayin da su kuma suka turo sunayen mutane 144,800 domin su wakilce su wajen lura da yadda zabukan za su wakana, zabukan da za a fara daga  ranar a Asabar 25 ga wata.

Haka kuma hukumar zaben ta tarayyar Najeriya ta tantance kungiyoyin kasashen wajen 33, inda su kuma suka turo mutane 2,113 domin sanya ido kan harkokin zabukan.

Wannan dai kamar yadda shugaban hukumar zaben ya bayyana shi ne karo na farko a tarihin zabukan Najeriya da aka samu adadin mai yawa na masu sanya idanu kan zabe.

Farfessa Mahmud Yakubu ya bukaci masu sanya idanun da su gudanar da aikin su bisa yadda yake kunshe cikin dokar sanya idon kan zabuka na duniya, inda ya kara nusantar da su cewa su yi kokarin tsayawa kan aikinsu na  masu sanya ido ba tare da su wuce gona da iri ba.

“A matsayin sunan da aka san ku da shi na masu sanya ido, ku yi kokarin dauke kanku daga nuna ra’ayin siyasa yayin da kuke gudanar da aiki, domin shi dai wannan zabe harka ce ta cikin gida, wajibi ne kuma ku martabar matsayin kasar nan a matsayin  kasa mai cin gashin kanta.”

Shugaban hukumar zaben ya kara jaddada cewa Najeriya ba za ta lamunci yin katsalandan daga wata kasa ba kan harkokin gudanar da zabuka, amma dai za ta yi marhabin da duk wasu shawarwari da za su taimaka mata wajen inganta damokuradiyya a dukkan matakai. (Garba Abdullahi Bagwai)