logo

HAUSA

Me Amurka ke kokarin nunawa Duniya?

2023-02-22 09:45:59 CMG Hausa

Duk mai bibiyar kafofin watsa labarai, ba zai rasa jin labaran da wani dan jaridar Amurka mai suna Seymour Hersh ya rubuta ba, inda a cikin rahoton nasa ya ban kado makircin Amurka na lalata bututun Nord Stream na Rasha dake jigilar iskar gas zuwa yankin Turai. Sai dai kamar yadda kowa ya sani, ma’aikatar harkokin wajen kasar da hukumar leken asirin kasar ta CIA, da fadar White House duk sun musunta hakan.

Ana cikin wannan ne kuma, sai wani jirgin kasa dauke da sinadarai masu guba ya goce daga layinsa, inda nan take ya kama da wuta, a garin New Palastine dake jihar Ohio. Bayanai na cewa, sinadaran da jirgin ya dauko ya malala cikin koguna dake kewaye tare da kashe daruruwan kifaye, har ma jama’a sun fara gamuwa da nau’o’i na rashin lafiya, kama daga zazzabi zuwa ciwon kai da sauran matsalar rashin lafiya dake da nasaba da numfashi, sakamakon hayakin da ya turneku sararin samaniya. 

Masana kiwon lafiya na fargabar cewa, lamarin ya iya haddasa matsalar kiwon lafiya nan da shekru 20 masu zuwa. Sai dai a nan ma, kafofin watsa labaran Amurka ba su ce komai ba kan wannan batu. Shin me Amurka ke kokarin nunawa duniya da irin wannan hali na neman wasa da hankalin jama’a? (Saminu/Ibrahim/Sanusi Chen)