logo

HAUSA

Da alamun samun horon kyautata karfin jiki yana taimakawa wajen yin barci

2023-02-21 08:20:48 CMG Hausa

Masu karatu, ga alama, tsawaita lokacin barci da mintoci 17 a ko wace rana, ba shi da yawa, ga wadanda suke yin dogon barci cikin kwanciyar hankali. Amma ga wadanda suke fama da matsalar yin barci, ko wadanda su ke yawan farka cikin dare, kara samun mintoci 17 a ko wace rana na yin barci, yana da matukar amfani.

To, akwai wani sakamakon nazari mai kyau ga wadanda ke fama da matsalar barci. An gano cewa, daukar abu mai nauyi ko kuma motsa jiki ta hanyar ruf da ciki, suna iya tsawaita lokacin barci da mintoci 17 a ko wace rana, gwarwadon gudu ko kuma hawan keke.

An gudanar da nazarin kan masu fama da matsalar kiba ko wadanda nauyin jikinsu ya wuce misali kilogram 386, ‘yan shekaru 35 zuwa 70 a duniya, wadanda suka saba da zama a kujera cikin dogon lokaci, suna fama da matsalar hawan jini.

An raba wadannan mutane zuwa rukunoni guda 4, wato rukunin mutanen da ba sa motsa jiki, rukunin wadanda suka shafe awoyi 3 a ko wane mako suna motsa jiki don kyautata karfin jiki, rukunin wadanda suka shafe awoyi 3 a ko wane mako suna gudu, da rukunin wanda suka motsa jiki don kyautata karfin jiki da kuma gudu duka. An bukaci dukkan mutanen su gabatar da rahotanni kan ingancin barci, tsawon lokacin barci da kuma tsawon lokacin da suke barci.

Masu nazarin sun lura da cewa, a cikin wadanda tsawon lokacin da suka dauka suna yin barci a ko wace dare bai wuce awoyi 7 ba, idan suna gudu ko hawan keke, to, za su samu karin mintoci 23 na yin barci a ko wane dare, yayin da wadanda suka motsa jiki don kyautata karfin jiki kuma, suka samu karin mintoci 40 na yin barci. Sa’an nan kuma, wadanda suka motsa jiki don kyautata karfin jiki, sun fi saurin yin barci. Duk wanda ya motsa jiki, yana samun kyautatuwar ingancin barci da kuma sassauta matsalar barci da suke fuskanta.

Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, motsa jiki na da matukar muhimmanci ga lafiyar dan Adam. Sakamakon nazarin ya sake nuna mana cewa, watakila motsa jiki don kyautata karfin jiki, ya fi dacewa da kyautata ingancin barci da dare.

Sakamakon nazarce-nazarce a baya-bayan nan, ya shaida cewa, matsalar karancin barci ko kuma yin barci maras inganci za su kara barazanar kamuwa da ciwon hawan jini, toshewar hanyoyin jini da dai sauransu. Haka kuma, matsalar karancin barci tana da nasaba da karuwar nauyin jiki, kamuwa da ciwon sukari da gyambon sassan jiki, tare da kara barazanar kamuwa da shan inna, ciwon zuciya ko kuma haddasa mutuwar mutane da bai kamata a ce sun mutu ba. (Tasallah Yuan)