logo

HAUSA

Sojoji 51 sun mutu yayin wani hari a arewacin Burkina Faso

2023-02-21 13:40:49 CMG Hausa

Rundunar sojan kasar Burkina Faso ta bayyana a jiya Litinin cewa, an kai hari a lardin Oudalan na yankin Sahel da ke arewacin kasar, inda sojoji a kalla 51 sun rasa rayukansu, yayin da aka harbe ‘yan ta’adda kimanin 160 yayin musayar wutar.

Wata sanarwar da rundunar sojan Burkina Faso ta fitar na cewa, an kai harin kwantar bauna kan wasu sojojin kasar, inda wasu 8 suka rasu, wasu 3 suka jikkata, yayin da wasu kuma suka bace. A yayin samammen da sojan kasar suka kai daga baya a wurin da harin ya auku, sun yi nasarar harbe ‘yan ta’adda 60, tare da lalata motoci masu sulke 7 da gomman babura.

A daren ranar 20 ga wata, rundunar sojan Burkina Faso ta sake ba da wata sanarwar cewa, an gano gawawwakin wasu sojoji 43, inda adadin sojojin da suka mutu ya kai 51. Mayakan saman kasar sun kara kai hari ta sama, inda suka halaka ‘yan ta’adda 100. (Tasallah Yuan)