logo

HAUSA

Abdulhafiz Hamza: Ina kira ga jama’a su yarda da labaran kafafen yada labaran kasar Sin

2023-02-21 15:44:11 CMG Hausa

Abdulhafiz Hamza, dan Kano ne wanda a yanzu haka yake ziyartar iyalinsa a Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Malam Hamza, wanda ya taba ziyartar kasar Sin sau da dama, ya zanta da Murtala Zhang, inda ya bayyana ra’ayin sa kan ci gaban da kasar Sin ta samu a fannoni daban-daban a wadannan shekaru.

Hamza, ya kuma yi kira ga al’ummar Najeriya, da su kara sauraren labaran da kafafen watsa labaran kasar Sin ke yadawa, maimakon saurin yarda da labaran da kafafen watsa labaran kasashen yammacin duniya ke kokarin yadawa, da zummar shafawa kasar Sin bakin fenti. Saboda a cewar sa, shi ganau ne ba jiyau ba, kuma ya taba ziyartar kasar Sin sau da yawa, inda ya ganewa idanunsa ainihin halin da ake ciki a kasar. (Murtala Zhang)