logo

HAUSA

Gaskiyar Danniyar Amurka

2023-02-21 14:07:26 CMG Hausa

A ranar 19 ga wata, agogon wuri, wasu masu adawa da yake-yake na kasar Amurka sun yi gangami a birnin Washington na kasar, inda suka bukaci Amurka da ta dakatar da taimakawa kasar Ukraine ta fuskar aikin soja, tare da yin kira da a wargaza kungiyar tsaro ta NATO. Duk da haka kwana guda bayan gangamin, wato jiya Litinin 20 ga wata, shugaba Joe Biden na Amurka ya kai wata ziyarar ba-zata zuwa Ukraine, inda ya sanar da kara bai wa Ukraine taimakon dalar Amurka miliyan 500, ciki had da makamai. Lamarin da ya nuna cewa, Amurka ita ce da ke da hannu wajen rura wutar rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine cikin shekara guda da ta gabata, wadda kuma ta fi yin danniya a duniya yanzu.

Rura wutar rikicin Ukraine, wani bangare ne na yunkurin Amurka na yin danniya a duniya a shekarun baya-bayan nan. Rahoton “yadda Amurka ke yin danniya da kuma illolinsa” da kasar Sin ta fitar jiya Litinin ya bayyana gaskiyar danniyar Amurka a fannonin siyasa, aikin soja, tattalin arziki, kimiyya da fasaha, da al’adu. Rahoton ya yi wa kasashen duniya karin bayani kan yadda Amurka take yin danniya a duniya da abubuwa na rashin kunya da take yi.

Daga tunzura a yi mulkin danniya a kasashen Turai da Asiya, zuwa kulla makarkashiyar yin juyin mulki a yammacin Asiya da arewacin Afirka, kullum Amurka tana yunkurin kafa tsari da oda a wasu kasashe da ma duniya baki daya, da sunan shimfida demokuradiyya da kiyaye hakkin dan Adam, amma hakika ba a samu demokuradiyya a wadannan yankuna da kasashe ba, sai tashin hankali da bala’u kawai. Demokuradiyya irin ta Amurka ba ta samu nasara ba.

Kullum Amurka tana sadaukar da tsaron wasu kasashe, dakile ci gaban wasu kasashe, da sadaukar da alherin al’ummun wasu kasashe, don neman yin danniya, da kiyaye yadda take yi, da kuma yin amfani da fifikonta. (Tasallah Yuan)