logo

HAUSA

Sin za ta yi aiki tare da sauran kasashe don gina duniya mai tsabta da kyan gani

2023-02-21 19:02:48 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Talatar nan cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya, don kara karfafa ra'ayin samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da gina duniya mai tsafta da kyan gani, da kafa rundunar hadin gwiwa mai karfi da za ta yi nasarar gina al'umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama.

A cewar ma'aikatar kula da muhalli, kasar Sin ta cimma nasarar burin kyautata yanayin muhallinta a shekarar 2022. (Ibrahim)