logo

HAUSA

Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce babban burin ta shi ne demokradiyya ta samu gindin zama a kasar

2023-02-21 09:15:04 CMG Hausa

A ranar Litinin 20 ga wata, hedikwatar tsaron Najeriya ta kara tabbatar da kudurinta na aiki tare da sauran hukumomin tsaron kasar wajen ganin an gudanar da babban zaben kasar cikin kyakkyawan yanayi na tsaro.

Yayin taron manema labarai da ya gabatar jim kadan bayan kammala taro da shugabanin hukumomin tsaron kasar a birnin Abuja, babban hafsan tsaron na tarayyar Najeriya General Lucky Irabor ya ce samun nasarar zabukan kasar nauyi ne da ya rataya a wuyan dukkan bangarorin tsaro.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.


Taron dai ya zo ne daidai lokacin da ya rage kwanaki 4 al`ummar kasar su fita domin sake zabar shugabannin da za su jagorance su yayin da wa’adin gwamnati dake kan mulki ke daf da karewa.

Taron wanda aka gudanar da shi a hedikwatar tsaron Najeriya ya sami halartar sufeto janar na ’yan sandan kasar da kuma daraktan sashen tsaron cikin gida na DSS da daraktan hukumar liken asiri ta kasa.

A jawabinsa babban hafsan tsaron Najeriya General Lucky Irabor ya ce manufar taron dai shi ne nazarin shirye-shiryen da aka yi ta fuskar tsaro domin zabukan dake tafe, sannan kuma a kara bullo  da wasu matakai da za su taimakawa wajen ganin an gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali.

Babban hafsan tsaron Najeriya ya ce duk da cewa kaso 80 na tabbatar da tsaro a lokacin zaben ya rataya a wuyan rundunar ’yan sanda ne, amma wannan ba zai hana sauran hukumomin tsaro su shigo cikin shirin ba musamman bisa la’akari da irin kalubalen tsaron da Najeriya ta shafe shekaru a cikinsa.

Sannan kuma shugaban hukumar zabe ta tarayyar Najeriya ya shigo da jami’an tsaro sosai cikin harkokin zabuka domin ganin cewar komai ya tafi dai dai ta fuskar tsaro.

“Ina kara tabbatar wa ’yan Najeriya cewa jami’an tsaro za su kasance a sahun gaba a duk wasu al’amura da za su saka natsuwa a zukatan su wajen fitowa domin sauke nauyin kasa da ya rataya a wuyansu na zabar shugabanni, sannan kuma mun shirya tsaf domin magani duk wani kalubale da ka iya afkuwa ta fuskar tsaro.”

Ha’ila yau kuma ya ja kunnen masu kokarin haifar da rikici yayin zabukan da cewa su shiga taitayin su, domin kuwa ba za su ji dadi ba idan har suka shigo hannun hukuma. (Garba Abdullahi Bagwai)