logo

HAUSA

Mutane dubu 600 suka samu allurar yaki da cutar ciwon wuya a Zinder

2023-02-21 09:17:31 CMG Hausa

A yankin Zinder na jamhuriyar Nijar, kungiyar “medecins sans frontieres” tare da hukumomin kiwon lafiya na kasa, ta yi wa mutane kusan dubu 600 allurar yaki da cutar ciwon wuya, da wasu kwayoyin cuta da ake shaka cikin iska ke janyo acisshewa da tari da kuma anago ga marar lafiya, har ya kai ga mutuwa. A tsakiyar watan Augustan shekarar 2022 ne, cibiyoyin kiwon lafiya suka shaida bullowar a garuruwan Tesker da Goure da ke cikin yankin Zinder, haka kuma a cewar hukumomin kiwon lafiya, wannan cutar Diphtérie mai haddasa ciwon wuya ta jima ba a same ta a kasar Nijar ba yau da shekara bakwai da suka gabata. Gaban wannan matsala ce, kungiyar MSF tare da hukumomin kasa, an bullo da wani shirin fuskantar wannan cuta ta hanyar bada kulawa da yin alluran rigakafi, musamman ma ta hanyar gudanar da kamfen shaushawa na jama’a domin ganin an kawar da wannan cuta kwata kwata daga cikin kasar Nijar.

A cewar rahoton MSF, likitar Tesker ta sanar da bullowar cutar tun daga ranar 20 ga watan Satumban shekerar 2022, sannan kuma ta bayyana a garin Goure. Zuwa ranar 22 ga watan Disamba, an gano mutane 40 da cutar ta harba, sannan mutane 14 suka mutu a Tesker, yayin da kuma a Goure, mutane 479 suka samu magani, sannan mutane 19 suka mutu. (Mamane Ada)