logo

HAUSA

An rufe taron koli karo na 36 na AU

2023-02-20 10:04:02 CMG Hausa

A daren jiya 19 ga wata agogon wurin ne, aka rufe taron koli karo na 36 na kungiyar tarayyar Afirka ta AU a babbar hedkwatar kungiyar da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. Inda aka tattauna kan batun tafiyar da harkokin yankin ciniki maras shinge na Afirka, zaman lafiya da tsaro, matsayin wakilcin kasashen Afirka a kungiyoyin kasa da kasa da dai sauransu, tare da nanata alkawarin kungiyar na warware matsalolin Afirka bisa karfin kanta.

A yayin bikin rufe taron, sabon shugaban karba-karba na kungiyar, kana shugaban kasar Comoros Azali Assoumani ya jaddada batutuwan gaggawa da ya kamata shugabannin kasashen Afirka daban daban su dora muhimmanci da kuma daukar alkawari a kansu. Inda ya nuna cewa, dole ne a tafiyar da harkokin yankin ciniki maras shinge na Afirka yadda ya kamata, ganin yadda yake da matukar muhimmanci ga ci gaban Afirka. Ban da wannan kuma Azali ya ce, shugabannin kasashen Afirka na kokarin fito da wani tsari don tabbatar da tsaro a kan teku, ta yadda za a iya ba da tabbaci ga zirga-zirgar jiragen ruwa yadda ya kamata yayin da ake tafiyar da harkokin yankin ciniki maras shinge na nahiyar.

Haka zakila, shugaban hukumar gudanarwar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat ya bayyana cewa, bisa matsayar da shugabannin kasashen Afirka suka cimma a gun taron, za a mai da hankali kan warware matsalolin rashin zaman lafiya da tsaro dake addabar kasar Libya, yankin Sahel, da kuma Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo. (Kande Gao)