logo

HAUSA

Kasar Faransa ta kammala aikin janye sojojinta na musamman daga Burkina Faso

2023-02-20 13:54:25 CMG Hausa

Babban hafsan sojojin kasar Burkina Faso da na rundunar sojojin musamman na Faransa, sun gudanar da wani bikin sauke tuta a sansanin da ke wajen birnin Ouagadougou, wanda ya alamta cewa dakarun musamman na Faransa a Burkina Faso sun kawo karshen aikinsu a hukumance.

Bisa jadawalin da bangarorin biyu suka tsara, wata tawagar ma'aikatan kula da tsare-tsare za ta kammala aiki tare da mika sauran makamai da kayayyakin aikin rundunar Faransa. 

A ranar 18 ga watan Janairu ne dai, gwamnatin rikon kwarya ta Burkina Faso ta yi Allah wadai da yarjejeniyar da aka cimma game da matsayin sojojin Faransa a kasar tare da ba su wa'adin wata guda da su fice daga kasar, a ranar 25 ga watan Janairu ne kuma bangaren Faransa ya amince da bukatar janyewar.

Rahotani na cewa, wadannan sojoji na musamman guda 400 na Faransa da aka jibge su a kasar Burkina Faso, za su koma kasashen Nijar ko Chadi wadanda suke makwabtaka da kasar Burkina Faso a kai a kai. (Safiyah Ma)