logo

HAUSA

Sharhi:Yadda Amurka ke wasa da hankalin al’umma

2023-02-20 14:58:05 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

A kwanakin baya, yadda wasu manyan abubuwan da suka faru a kasar Amurka sun jawo hankalin kasa da kasa. Na farko shi ne yadda wani jirgin kasa ya kauce daga layin dogon da yake bi a jihar Ohio ta kasar, na biyu shi ne yadda ake zargin gwamnatin Biden da tsara shirin lalata bututun iskar gas da ke tsakanin Rasha da Turai, na uku kuma shi ne yadda kasar Amurka ta harbo wani balan-balan na kasar Sin da makami mai linzami, sai dai yadda gwamnatin kasar Amurka ke mayar da martani ga batutuwan da ma yadda kafofin watsa labarai na kasar ke ba da rahotanni suna ba jama’a mamaki.

Jirgin kasan da ya kauce daga kan layin dogo yana dauke da sinadarai masu guba, lamarin da ya gurbata muhallin wurin sakamakon yadda sashen kula da al’amuran gaggawa na wurin ya daidaita hadarin, inda mazauna wurin suka fara ciwon kai da nuna sauran alamu na rashin lafiya, baya ga kuma dimbin kifayen da aka gano sun mutu a cikin kogunan wurin. A sa’i daya kuma, sanannen dan jarida na kasar Seymour Hersh ya fitar da wani rahoton bincike, inda ya zargi gwamnatin Joe Biden da lalata bututun jigilar iskar gas na Nord Stream, don neman cimma moriyar kanta. Wadannan manyan abubuwa ne da suka shafi rayuwar al’ummar kasar Amurka da ma sunan kasar, amma abin mamaki shi ne, gwamnatin Amurka da kuma manyan kafofin yada labarai na kasar duk sun yi shiru, a yayin da kuma suke ta rura wutar batun wai “balan-balan na kasar Sin”.

Shin me ya faru ga gwamnatin Amurka da kafofin watsa labarai na kasar? Me ya sa suke iya ganin balan balan da ta ratsa sararin samaniyar kasar bisa kuskure wanda ke da tsayin mita 18,000 daga doron duniyarmu,  amma sun kasa ganin gurbatacciyar hayakin da ke saman jihar Ohio? Me ya sa suke ta rura wutar zancen barazana daga sauran kasashe, amma kuma suka kawar da ido daga hakikanin abin da ke barazana ga lafiyar al’ummar kasar? Me ya sa a farkon fashewar bututun Nord Stream, suka daga murya suka ce dole a hukunta wadanda suka aikata laifin, amma kuma suka yi shiru bayan da Seymour Hersh ya fitar da rahotonsa?

   A game da wannan, mai fashin baki kan harkokin siyasar kasar Amurka Alex Krainer ya yi nuni da cewa, lokacin da Amurka ke kokarin rura wutar batun “balan-balan na kasar Sin, a daidai lokacin ne da jirgin kasan ya kauce daga kan layin dogo da kuma Seymour Hersh ya fitar da rahotonsa, kuma dalilin da ya sa ta yi hakan shi ne don kawar da hankalin al’umma daga hakikanin matsalolin da suke fuskanta.

To, ashe wasa da hankalin al’umma ke nan Amurka ke yi. (Mai zane:Mustapha Bulama)