logo

HAUSA

Jami’in MDD: fasahohin Sin za su taimaka wa Afirka tinkarar matsalar sauyin yanayi

2023-02-20 10:12:55 CMG Hausa

An gudanar da taron koli karon kungiyar tarayyar Afirka ta AU karo na 36 a birnin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha daga ranar 18 zuwa 19 ga wata. Inda Ibrahima Cheikh Diong, mai ba da taimako ga babban sakataren MDD, kana babban daraktan ofishin tinkarar matsaloli na Afirka na majalisar ya bayyana cewa, Afirka na fama da mummunar illa sanagiyar sauyin yanayi, kuma kyawawan fasahohin da kasar Sin ta samu a fannin tinkarar sauyin yanayi za su taimaka wa Afirka sosai.

Ibrahima ya kara da cewa, yanayi mai makukar tsanani na addabar nahiyar Afirka, bala’in ambaliyar ruwa da ya faru a kasashen Afirka ta Kudu, da Najeriya, da Nijar ya kawo illa sosai ga al’ummunsu, musamman ma mutane marasa karfi. Dimbin mutane sun rasa rayukansu da abubuwa da suka dogaro a kai sakamakon matsalar karancin abinci wadda sauyin yanayi ya haddasa.

Bugu da kari, Ibrahima ya ce, akwai bukatar a dauki matakai a duk fadin duniya wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi, kuma ofishinsa na hadin kai tare da kasar Sin. A cewarsa, kasar Sin na da kwarewa sosai wajen daidaita matsalolin sauyin yanayi da bala’u daga indallahi, kuma za ta iya taimakawa Afirka a fannonin fasahohi da aikin kara karfin tinkarar sauyin yanayi, ta yadda kasashen Afirka za su samu kwarewa a wannan fanni. (Kande Gao)