logo

HAUSA

An kammala aikin ceto a larduna takwas da girgizar kasa ta shafa a Turkiyya

2023-02-20 15:00:39 CMG Hausa

Hukumar kula da iftila’i da agajin gaggawa ta kasar Turkiyya ta bayyana a jiya da dare cewa, an kammala aikin ceto a larduna takwas da mummunar girgizar kasa ta shafa, ban da sauran larduna biyu da suka hada da Kahramanmaras da kuma Hatay. A mataki na gaba, za a mai da hankali a kan gina gidajen kwana na wucin gadi tare da farfado da muhimman kayayyakin more rayuwa. (Lubabatu)