logo

HAUSA

Kafa dokokin da suka dace ya taimakawa kasar Sin wajen samun babban ci gaba a sha'anin harkokin matan kasar

2023-02-20 20:25:55 CMG Hausa


“Ba za a samu ci gaba ba tare da mata ba, kuma dole ne kowa ya amfana da alfanun da hakan zai kawo”, cewar Shugaban kasar Sin Xi Jinping, yayin taron shugabannin duniya kan daidaiton jinsi da karfafa gwiwar mata, a hedkwatar MDD dake birnin New York na Amurka a ranar 27 ga watan Satumban 2015. Hakakika, tun daga shekarar 2012, kasar Sin ta fara bada matukar muhimmanci ga raya harkokin da suka shafi mata, kuma tana tabbatar da mata samun ‘yancinsu na demokradiyya, da shiga ana damawa da su cikin harkokin raya tattalin arziki da zamantakewa da kuma cin gajiyar sakamakon gyare-gyare da ci gaban kasa bisa daidaito da tanadin shari’a.

Cikin shekaru 10 da suka gabata, Sinawa mata sun yi kokarin shiga muhimman ayyuka da zama jakadun wayewar kai da kuma jagorori wajen cimma burikansu ta sabbin hanyoyi.

Wang Xiling, wadda ta samu lambar yabo ta kasa a yaki da talauci, ta ce “abu mafi muhimmanci shi ne, tsayawa da kafarka.” A lokacin da ta sauya daga ‘yar kauye mai fama da talauci, zuwa shugabar kungiyar gammaya kan aikin gona, ta gano cewa, ta cimma burinta na zama ‘yar kasuwa ne saboda damammakin da sabon zamani ya gabatar.

Tun bayan taron wakilan JKS na 18 da aka yi a shekarar 2012, muhimmin umarnin da shugaba Xi ya bayar kan mata da ayyukan matan, ya saita alkiblar ci gaban harkokin mata a kasar Sin, musamman a sabon zamani.

An rubuta alkawarin nacewa ga manufar kasar ta tabbatar da daidaiton jinsi da kare halaltattun hakkoki da muradun mata da yara, cikin rahotannin tarukan wakilan jam’iyyar karo na 18 da na 19.

Haka kuma, shawarar da aka yanke yayin zama na hudu na taron kwamitin tsakiya na JKS, ya jaddada kudurin jam’iyyar na daukakawa da inganta tsare-tsare da dabarun inganta daidaiton jinsi da ci gaban harkokin mata ta kowacce fuska. Kudurin kwamitin tsakiyar jam’iyyar kan manyan nasarori da gogewar da jam’iyyar ta samu cikin shekaru 100 da suka gabata, wanda aka amince da shi yayin zama na 6 na taron kwamitin tsakiyar karo na 19, ya nanata kudurin jam’iyyar na taimakawa wajen karfafa zumunci tsakanin iyalai da akidu da al’adu, da kuma kyautata kare hakkoki da muradun mata da yara.

Shirin raya tattalin arziki da zamantakewar kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13, tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, da irinsa karo na 14 da za a aiwatar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, sun kunshi shirye-shiryen inganta harkokin mata da yara da iyalai, kuma wadannan shirye-shirye sun taimaka wajen shimfida tubali mai kwari na inganta ci gaban harkokin mata, wadanda suka yi daidai da na raya tattalin arziki da zaman takewa.

Kwamitin kula da harkokin mata da yara karkashin majalisar gudanarwar kasar Sin ya tsara wani shirin kasa, na raya harkokin mata tsakanin shekarar 2021 zuwa 2030, inda kwamitin ke saita wasu muradu da dabarun raya harkokin mata a fannonin kiwon lafiya da ilimi da tattalin arziki da sauran wasu fannoni. Kwamitin mai kula da mata da yara a dukkan matakai, ya inganta aiwatar da wannan shiri. An kuma karfafa dabarun inganta harkokin mata wadanda suka kunshi jagorancin kwamitocin jam’iyyar da hakkokin da suka rataya a kan gwamnatoci da hadin gwiwa tsakanin kwamitocin kula da yara da mata da sauran sassan gwamnati tare da damawa da dukkan kungiyoyin al’umma.

Kasar Sin ta yi ta karfafa harkokin shari’a da suka shafi daidaiton jinsi da hakkoki da muradun mata. Ta kuma kafa wani tsarin shari’a, wanda ya kunshi dokoki da ka’idoji 100, domin su ba da cikakkiyar kariya ga hakkoki da muradun mata. Sabuwar dokar da ake kira da Civil Code, wadda ta fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun 2021, ta jaddada ba mata kariya a gidajen aure da kuma cikin iyali.

Dokar hana cin zarafin mata ta jamhuriyar jama’ar kasar Sin, wadda ta fara aiki a ranar 1 ga watan Maris din 2016, ta kare hakkokin mata a cikin iyali. Dokar inganta ilmantar da iyali ta jamhuriyar jama’ar kasar Sin, wadda ta fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun 2022, ta bayyana cewa, gwamnati da makarantu da al’umma, su bayar da jagoranci da goyon baya ga hidimar ilmantar da iyali.

Ita kuwa dokar yarjejeniyar filaye a yankunan karkara ta kasar Sin, an yi mata gyaran fuska a 2018, domin inganta dokokin kare hakkokin mata kan filaye a yankunan karkara. An kuma kafa dabarar tantance yanayin daidaiton jinsi a matakan kasa da na larduna 31 da yankunan masu zaman kansu ko birane, domin karfafa dokokin kare hakkoki da muradun mata.(Kande Gao)