logo

HAUSA

Jirgin kasa dake zuwa wurin wasan kankara

2023-02-19 18:34:55 CMG Hausa

Garin Altai dake arewacin jihar Xinjiang, ya shahara sosai a fannin samun muhalli na musamman, wanda ya dace da gudanar da wasannin kankara. Saboda haka, a lokacin sanyi, a kan samu dimbin mutane masu sha’awar wasannin kankara, irinsu skiing da snowboard, wadanda ke kama hanyar zuwa Altai don neman jin dadin wasannin. Sai dai nisan dake tsakanin Urumqi, hedkwatar jihar Xinjiang, da garin Altai, ya kai fiye da kilomita 900. Don haka mai yiwuwa mu yi tunanin ta yaya za a iya samar da sauki ga mutanen dake son zuwa Altai? To, don biyan wannan bukata, an kaddamar da wani sabon jirgin kasa na musamman, mai lamba Y965. (Bello Wang)