logo

HAUSA

An kori babbar jami'ar diflomasiyyar Isra'ila daga taron AU

2023-02-19 16:07:47 CMG Hausa

A jiya ne aka kori wata babbar jami’ar diflomasiyyar Isra’ila daga taron shekara-shekara na kungiyar Tarayyar Afirka(AU) da aka bude a kasar Habasha, a gabar da takaddama kan amincewar Isra’ila a cikin kungiyar ta karu.

Wasu hotunan da aka wallafa a shafin yanar gizo, sun nuna jami'an tsaron AU suna arangama da jami'ar diflomasiyyar a yayin bikin bude taron, kafin ta fice daga dakin taron.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Isra'ila ta bayyana cewa, Isra'ila ta yi kakkausar suka kan lamarin da ya faru, bayan da aka kori mataimakiyar darakta mai kula da Afirka, jakadiya Sharon Bar-Li daga zauren kungiyar Tarayyar Afirka, duk da matsayinta na 'yar kallo da aka amince da ita da kuma bajin shaidar shiga dakin taron.

Ebba Kalondo, kakakin shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka, ta ce an kori jami'ar diflomasiyyar ce, saboda ba ita ce jakadiyar Isra'ila da aka amince da ita a Habasha ba, jami'in da ake sa ran zai halarci taron.

Sai dai Isra'ila ta dora alhakin lamarin a kan kasasen Afirka ta Kudu da Aljeriya, kasashe biyu masu muhimmanci a cikin mambobin kasashe 55 na kungiyar, inda ta ce, suna dora laifin kan kungiyar ta AU. (Ibrahim)