logo

HAUSA

Wace fa’ida AfCFTA za ta haifar wa Najeriya?

2023-02-19 20:56:29 CMG Hausa

A kwanakin nan, an bude taron shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka ta AU a Addis Ababa, inda aka sanya wa taron taken “ gaggauta gina yankin ciniki cikin ‘yanci na Afirka (AfCFTA)”.

To, dangane da yankin AfCFTA, na tuna akwai wani abokina da ya tambaye ni ta shafin Facebook, cewa mene ne amfanin yankin ga Najeriya? Don amsa wannan tambaya, ina so in yi amfani da kanju wajen ba da misali.

Sanin kowa ne, ana samun kanju mai inganci a kasar Najeriya. Sai dai kusan ba a ganinsu a kasuwannin kasar Sin. To, mene ne dalili? Saboda kasashen kudu maso gabashin Asiya dake makwataka da kasar Sin, su ma suna samar da dimbin kanju masu inganci. Idan an kwatanta da kanju din kasar Najeriya, kudin jigilar kanju daga wadannan kasashen zuwa cikin kasar Sin ya fi araha. Kana wani abu mai muhimmanci shi ne, kasar Sin da mambobin kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya (ASEAN) sun kulla yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci, inda kasashen ASEAN da dama suke iya fitar da kanju zuwa kasuwannin Sin ba tare da biyan kudin kwastam ba. Wadannan sharuda sun sa kanju din kasashen kudu maso gabashin Asiya sun fi araha a kasuwannin kasar Sin, abin da ya sa suka fi samun karbuwa.

Yanzu tun da an kafa yankin AfCFTA, gami da kulla yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci a nahiyar Afirka, za a iya cin gajiyar kudin jigilar kaya mai araha, da soke kudin kwastam, yayin da ake fitar da kanju na kasar Najeriya zuwa sauran kasashen dake nahiyar Afirka, ta yadda kanjun kasar Najeriya zai kara samun karbuwa a kasuwannin kasa da kasa. Ban da wannan kuma, idan an samu karuwar kanjun da kasar Najeriya ke fitar zuwa ketare, kamfanonin sauran kasashe, misali, na kasar Sin, za su so su zuba jari a ma’aikatun sarrafa kanju na kasar Najeriya, don habaka harkarsu ta samar da kanju. Ta haka, masana’antun kasar za su samu ci gaba, tare da samar da karin guraben aikin yi. Hakan ma abun yake idan aka dauki misali da sauran kayayyakin kirar Najeriya.

Ban da haka, don raya aikin ciniki, ba za a rasa kayayyaki more rayuwa masu inganci, musamman ma ta fuskar aikin sufuri ba. A wannan fanni, Najeriya ta samu sharadi mai kyau, albarkacin hadin gwiwarta da kasar Sin cikin dimbin shekarun da suka gabata. Idan ba a manta ba, cikin wadannan shekaru, kamfanonin kasar Sin sun kammala ayyukan gina wasu manyan kayayyakin more rayuwa masu yawa a kasar Najeriya, wadanda suka hada da layin dogo da ya hada Abuja da Kaduna, da layin da ya hada Lagos da Ibadan, da karamin layin dogo na Abuja, da sabon ginin dake cikin filin saukar jiragen sama na Abuja, da tagwayen hanyoyi na Badagari, da dai sauransu. Ko a cikin wannan shekara ma, an kaddamar da tashar jiragen ruwa ta Lekki, da karamin layin dogo na Blue Line dake birnin Lagos. Wadannan kayayyaki za su zama tushen ci gaban tattalin arzikin kasar Najeriya, ta la’akari da yadda ake raya yankin AfCFTA a nahiyar Afirka.

Idan mun dauki tashar jiragen ruwa a matsayin misali. A kwanakin baya, na ziyarci biranen Ningbo da Jinhua dake gabashin kasar Sin. Dukkansu birane ne dake lardin Zhejiang, wadanda suke kusa da juna, kana sun yi suna a fannin yanayin ciniki mai armashi. Idan an kwatanta yawan al’ummarsu, za a ga a Ningbo akwai mutane miliyan 9.54, yayin da yawan al’ummar Jinhua ya kai miliyan 7.12. Sai dai darajar kudin kayayyakin da ake samarwa a duk shekara na GDP na birnin Ningbo, ya ninka na Jinhua har kusan sau 3. Saboda me? To, wani babban dalilin da ya sa haka, shi ne domin Jinhua yana dab da duwatsu, yayin da Ningbo yana bakin teku, yana kuma da tashar jiragen ruwa mafi girma a duniya. Wannan batu ya nuna muhimmancin tashar jiragen ruwa. Yanzu girman jirgin ruwan da tashar Lekki za ta iya dauka, ya ninka na tsoffin tashoshin jiragen ruwa na kasar Najeriya har sau 4, kana tashar za ta iya karbar kwantainoni miliyan 1.2 a duk shekara, wanda yake kan gaba cikin dukkan tashoshin jirgin ruwa na yammacin Afirka. Abun da za mu yi la’akari da shi yanzu, shi ne bisa kokarin da ake yi na raya yankin ciniki cikin ‘yanci na AfCFTA, kasar Najeriya za ta ci gajiyar manyan tashoshin jiragen ruwa, da sauran kayayyakinta na more rayuwa, da wata hadaddiyar babbar kasuwa ta daukacin nahiyar Afirka, inda za ta zama wata muhimmiyar cibiyar ciniki da ta hada nahiyar Afirka, da sauran sassan duniya.

A ganina, kuma bisa matsayina na Basine, na ga shirin AfCFTA da shawarar kasar Sin ta gina wata al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya suna da ma’ana iri daya, inda dukkansu sun nuna bukatar samun cudanya, da hadin gwiwa, da moriyar bai daya, tsakanin kasashe da al’ummu daban daban, gami da muhimmancin kula da al’amura ta hanyar yin shawarwari da tattaunawa, da raba moriya cikin daidaito, gami da samun ci gaba tare. A nan gaba, za a ga yadda shirin nan na AfCFTA zai amfani kasar Najeriya, da sauran kasashen dake nahiyar Afirka, gami da baiwa daukacin kasashen duniya damar samun karin ci gaba. (Bello Wang)