logo

HAUSA

Guterres: Afirka na fama da matsalar sauyin yanayi, rashin daidaito da matsalar abinci

2023-02-19 16:11:30 CMG Hausa

 

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, kalubale masu alaka da juna na tunkarar duniyarmu, inda nahiyar Afirka za ta fuskanci manyan kalubale.

Guterres ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a babban taron kolin kungiyar Tarayyar Afirka (AU) karo na 36 jiya Asabar a Addis Ababa,babban birnin kasar Habasha. Yana mai cewa, kwanan nan ya yi jawabi ga babban taron MDD kan kalubale iri-iri, masu alaka da juna da ke fuskantar duniyarmu fiye da kowanne lokaci a cikin rayuwarmu

Ya ce, tsarin hada-hadar kudi na duniya ba ya aiki ga rashin adalci da ke yiwa kasashe masu tasowa illa, da rashin daidaito mai zurfi da kuma karancin albarkatun da za a iya yin amfani da su don samun murmurewa daga annobar COVID-19 na daga cikin manyan kalubalen da nahiyar Afirka ke fuskanta.

Ya bayyana cewa, matsalar tsadar rayuwa, sanadiyar rikicin Ukraine da matsalar sauyin yanayi, suna kara jefa al'umma da rayuka cikin hadari tare da raba miliyoyi da muhallansu.

Guterres ya jaddada bukatar kasashe masu tasowa, su kasance masu karfin fada a ji a cibiyoyi na duniya, ciki har da kwamitin sulhu na MDD. Yana mai cewa, ya kamata kasashe masu tasowa, su samu bakin fada aji a cibiyoyin duniya, ciki har da cibiyoyin kudi, da kwamitin sulhu,da tsarin Bretton Woods, wannan wani misali ne na musamman inda nahiyar Afirka ba ta da wakilci. (Ibrahim)