logo

HAUSA

Xi Jinping ya aika da sakon murnar kiran taron kolin AU karo na 36

2023-02-18 17:44:53 CMG Hausa

Yau 18 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sako ga taron koli karo na 36 na kungiyar tarayyar Afirka AU don taya kasashen Afirka da al’ummunsu murnar bude taron.

Xi ya nuna cewa, a cikin shekarar da ta gabata, AU ta jagoranci kasashen Afirka wajen tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, da gaggauta aikin raya yankin ciniki maras shinge na Afirka, da taka muhimmiyar rawa wajen daidaita matsalolin nahiyar da suka jawo hankalin duniya. Lamarin da ya taimaka wajen daga matsayin kasashen Afirka da tasirinsu a duniya. Don haka Sin na fatan kasashen Afirka da al’ummunsu za su kara samun nasarori a kan hanyar samun bunkasuwa da farfadowa.

Kana shugaba Xi ya jaddada cewa, yana son yin aiki tare da shugabannin kasashen Afirka wajen inganta hadin kai na aminci a tsakanin bangarorin biyu, da kara hada kai wajen daidaita harkokin duniya da na shiyya-shiyya, a kokarin kara raya makoma ta bai daya a tsakanin Sin da Afirka.(Kande Gao)