logo

HAUSA

Dabarar Siyasa Ta Balan-balan Ta Amurka

2023-02-18 22:03:17 CMG Hausa

Kwanan baya, shugaban kasar Amurka ya furta a fadar White House cewa, babu alamar da ke nuna cewa, akwai wata alaka a tsakanin abubuwa guda 3 da aka harbo daga sararin sama da kuma kasar Sin. Amurka za ta ci gaba da tuntubar kasar Sin, don kaucewa barkewar sabon yakin cacar baka a tsakanin kasashen 2. Duk da haka, ya yi shelar cewa, kasarsa ba za ta nemi gafara kan yadda ta harbo balan-balan din kasar Sin ba.

Wannan shi ne dabarar wasu Amurkawa wajen daidaita batun balan-balan din. Amurka ta nemi kare kanta kan harbo balan-balan din kasar Sin, tare da ci gaba da nuna ra’ayin rikau kan kasar Sin. Amma kowa ya gane cewa, Amurka ba ta nuna sahihanci ba, ba ta lalubo hanyar warware batun ba.

Yadda wasu Amurkawa suka shafa wa kasar Sin bakin fenti domin samun moriyar siyasa cikin takarar jam’iyyu, ya sanya duniya ta ga abubuwan da Amurka ta aikata. Mahukuntan kasar Sin sun bayyana cewa, tun daga watan Mayun shekarar 2022 da ta gabata, Amurka ta bar balan-balan masu dimbin yawa suna shawagi a sararin samaniyarta, wasu daga cikinsu sun shiga samaniyar kasar Sin a kalla sau 10 ba bisa doka ba. Me ya sa Amurka ba ta ce kome ba kan lamarin, amma ta dauki matakin da bai dace ba kan kumbun farar hula na kasar Sin da ya shiga samaniyar ta bisa kuskure? Amurka ta sake nuna fuska biyu, kamar yadda ta saba yi a baya. (Tasallah Yuan)