logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun hakala ‘yan bindiga 7 a wani samame da suka kai

2023-02-18 15:22:01 CMG Hausa


Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna a tarayyar Najeriya, Samuel Aruwan ya bayyana cewa, a baya-bayan nan sojojin Najeriya, sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga a kalla 7 a wani samame da suka kai a jihar da ke arewacin kasar.

Aruwan ya bayyaa hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Jumma’a, inda ya ce, an gudanar da farmakin ne tare da hadin gwiwar dakarun sojin kasa da na ruwa a kusa da wani kogi a karamar hukumar Chikun dake jihar. Sai dai bai bayyana ainihin lokacin da aka gudanar da samamen ba.

Jami’in ya bayyana cewa, bayanan da gwamnatin jihar ta bayar sun nuna cewa, sojojin sun fara kai farmakin ne tare da tuntubar ‘yan ta’addan da ke kusa da kogin, inda nan take suka shiga tare da fatattakar ‘yan bindigar bayan da suka yi harbin mai tsanani.

A yayin samamen, sojojin sun kwato babura guda 5, da harsasai 153, da jigidar harsasai 7, da wayoyin hannu guda 3 duk daga hannun ‘yan fashin. (Ibrahim)