logo

HAUSA

Xi Jinping ya damu da gadon al’adun kasar Sin (4): Zhengding na da da yanzu

2023-02-18 21:28:51 CMG Hausa

 

A lokacin bazara na shekarar 1982, Xi Jinping, wanda bai kai shekaru 29 da haihuwa ba a lokacin, an nada shi mataimakin sakatare kuma sakataren kwamitin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a gundumar Zhengding na lardin Hebei.

Ya kasance mai sha'awar tarihin Zhengding, lokacin da ya isa Zhengding, tsoffin gine-ginen da ke wurin gami da manyan al’adun gargajiya, sun jawo hankalinsa matuka. Ya karanta tarihin gundumar da kayan tarihi, ya yi tattaki a kan tituna da lunguna tare da duba abubuwan tarihi.

A lokacin da yake aiki a Zhengding, ya yi aiki tukuru don inganta aikin ceto da kare kayayyakin al'adu. Godiya ga kokarinsa, martabar kayayyakin al'adu na Zhengding sun dawo.

Xi Jinping ya ce, "abubuwan tarihi na dauke da kyawawan wayewa, suna gadon tarihi da al'adu, da kuma raya ruhin kasa, wadannan su ne muhimmin al'adun gargajiya da kakanninmu suka bar mana."