logo

HAUSA

Xi Jinping ya damu da gadon al’adun kasar Sin (5): Sabuwar surar tabkin Xihu

2023-02-17 20:28:15 CMG Hausa

Kyawun tabkin Xihu ya haye tasirin duk wani irin yanayi. A cikin sama da shekaru 2,000, an fara aiwatar da manyan ayyuka sama da 20 domin ceton tafkin Xihu daga bacewa daga doron kasa. A farkon shekarar 2002, wadda ita ce shekara ta farko ta mulkin Xi Jinping a birnin Zhejiang, an kuma kaddamar da aikin ba da kariya ga tabkin a hukumance.