Ramin dutse mai lamba 172 na Dunhuang
2023-02-17 08:59:46 CMG Hausa
Tun daga shekarar 2017, Han Weimeng da tawagarsa suka shagaltu da gyarawa da kwafi da kuma nazari kan ramin dutse mai lamba 172 na Dunhuang. Ramin dutsen mai lamba 172 yana da tarihi na kimanin tsawon shekaru 1,200, kuma ya kasance alama ta daular Tang mai wadata a kasar Sin. Ta hanyar yin hadin gwiwa tare da sashen kimiyya da fasaha na kare kayayyakin al'adu, tawagar ta yi amfani da hanyoyin nazari irin na kimiyya don ganin cikakkun bayanan zane-zanen dake kan bangon ramin wadanda idanun dan Adam ba zasu iya gani ba. Han Weimeng da tawagarsa na fatan cewa nan gaba kadan za a iya nuna ainihin zane-zanen bango na ramin dutse mai lamba 172 ga duk duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)