logo

HAUSA

Masanin Najeriya: Lalata bututun Nord Stream da Amurka ta yi ya saba wa tsarin dokokin MDD

2023-02-17 11:28:13 CMG Hausa

Dangane da rahoton bincike kan bututun iskar gas na "Nord Stream" wanda babban dan jaridar Amurka Seymour Hersh ya wallafa, wani masani dan Najeriya mai suna Pau Gwaza ya bayyana a kwanan baya cewa, bai kamata wata kasa ta lalata abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum da jin dadin jama'a a wasu yankuna ba, domin cimma muradunta kawai, kuma ya kamata kasashen duniya su bayyana adawarsu tare da kaddamar da bincike game da lamarin.

Paul Gwaza, mai aikin bincike a cibiyar Nazarin Zaman Lafiya da Rikici ta Najeriya ya ce, lalata bututun iskar gas, da katse jigilar hatsi, don hana mutane samun abinci da makamashi, duk wadannan abubuwan da kasar Amurka ta yi sun lalata muhimman ka'idojin da aka amince da su a Majalisar Dinkin Duniya. Don haka bai kamata Amurka ta aikata abubuwan da suka saba wa muhimmiyar kimar tsarin dokoki na Majalisar Dinkin Duniya ba, irin wadannan matakan da duk wata kasa da ke dauka suna kawo cikas wajen tabbatar da hakkin bil’adama, don haka, bai kamata a aikata su ba. A cewar masanin, dole ne kasashen duniya su gano kasar da ta lalata bututun iskar gas din, kuma bisa ga wannan yanayin da muke ciki, kasar da muke magana akan ta ita ce Amurka. (Mai fassara: Bilkisu Xin)