logo

HAUSA

Ba zai yiwu a samu hadarin kaucewar jiragen kasa da yawa daga kan layin dogo a lokaci guda ba

2023-02-17 13:54:55 CMG Hausa

"Yadda ake samun kaucewar jiragen kasa da yawa daga kan layin dogo a lokaci guda, wannan abu ne da ba zai yiwu ba, dole ne akwai wani abu a kasa!" A shafukan sada zumunta na Amurka, mutane sun nuna shakku kan wannan batu daya bayan daya. A halin yanzu, hadarin "jirgin kasa dake dauke da sinadarai masu guba" da ya faru a Ohio na kasar Amurka yana ci gaba da jawo hankulan mutane, amma yayin da al’ummar yankin ke ci gaba da zaman fargaba da kuma mamakin aukuwar hakan, irin wannan hatsarin jirgin kasa ya afku daya bayan daya a Texas da South Carolina.

Sakamakon sabon binciken da Hukumar Kula da Sufuri ta Amurka ta fitar a ranar 14 ga wata, ya bayyana cewa, watakila an samu hadarin kaucewar jirgin kasa daga kan layin dogon a Ohio ne saboda zafin tsarin lura da sassan wilin jirgin kasan. Amma, a hakika, wannan hadarin jirgin kasa ya auku ne sakamakon kokarin neman riba mai yawa da kamfanin na layin dogo ke yi na tsawon shekaru, wanda ke haifar da tarin hadurra.  Wannan ya kara nuna yadda dukkan tsarin layin dogo na Amurka ke neman moriya kawai amma ba tare da la'akari da saura ba. Haka ya fallasa manyan matsalolin ci gaba da ake da su.

A ganin manyan kamfanonin jiragen kasa masu jigilar kayayyaki na Amurka, aikin farko na layin dogo shi ne "kayan aiki na samun karin kudi", amma ba "mahimman ababen more rayuwa" ba. Lokacin da tsarin jirgin kasa ya cika da "neman kudi", to hadarin yana karuwa kuma nan da nan. Idan komai ya dogara da manufar samun riba, komai yawan tsare-tsaren ababen more rayuwa da Amurka ta gabatar, da kyar suke iya amfanar talakawa.

Ga 'yan siyasar Amurka, idan ba su yi kwaskwarima sosai kan tsare-tsare ba, duk wani kyakkyawan tsarin samar da ababen more rayuwa ba shi da wani amfani, illa wata dabara ta karkatar da kasafin kudi zuwa aljihun manyan jami’an kamfanoni. To, ta yaya za su ba da amsa kan “Yadda Amurka ta zama haka?”  (Mai fassara: Bilkisu Xin)