logo

HAUSA

Muhammadu Buhari: Sauyin kudade da aka yi a kasar daya ne daga matakan tabbatar da tsaro da yaki da cin hanci

2023-02-17 09:54:17 CMG Hausa

A ranar Alhamis 16 ga wata, yayin jawabi da ya yi wa al’ummar kasar, shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, sauyin kudade da aka yi a kasar daya ne daga cikin matakan da ake bi wajen tabbatar da tsaro da yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma.

A jawabin da ya yi ta kafofin yada labarai na kusan tsawon rabin sa’a da safiyar Alhamis, shugaba Muhammadu Buhari haka kuma ya ce kokarin ta da komadar tattalin arziki da kuma kawar da munmunan kallon da kasashen duniya ke yiwa ’yan Najeriya shi ma yana daga cikin manyan dalilai da suka tilastawa gwamnati sauya nau’in wasu kudaden kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban kasar ya ce, wani abu yau kusan watanni biyu da fara aiwatar da sauyin kudade da babban bankin kasar ya bullo da shi, lamarin da akasarin ’yan Najeriya kuma ke kokawa sakamakon matsin rayuwar da shirin ya jefa su a ciki.

A jawabin nasa, shugaba Buhari ya fara da bayyana damuwarsa bisa yanayin da sauyin kudin ya jefa al’ummar kasar duk da dai gwamnati ta bullo da tsarin ne da kyakkyawar manufa ta kara bunkasa tattalin arziki da maido da darajar kudin kasar wanda suke fuskantar barazana a kasuwar canjin kudade ta duniya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce tun a zangonsa na farko yake da manufar farfado da tattalin azikin kasar wanda kuma hakan ta ba shi damar bin matakai daban daban bisa shawarwarin kwararru da masu ruwa da tsaki.

Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya shafe shekaru yana cin karo da kalubalen masu debe dukiyar kasar suna boyewa a kasashen waje, da kuma wadanda suke rike kudaden kasar ba tare da ana juya su cikin bangarorin tattalin arziki ba.

Shugaban ya ci gaba da cewa babu yadda za a yi a sami ci gaban tattalin arziki a irin wannan yanayi.

“A shekara ta 2015, kaso 78 na adadin kudin kasar yana hannun al’umma ne sabanin bankuna yayin da kuma a shekara ta 2022 adadin ya haura zuwa kaso 85. A watan Oktoban shekarar bara kudaden da gwamnati ta  saki sun kai tiriliyon 3.28 wanda daga cikin wannan adadi Naira biliyan 500 ne kawai suke a cikin bankuna yayin da tiriliyan 2.7 suke a hannun wasu daidaikun jama’a wanda wannan shi ne yake shafar tattalin arziki da kuma hauhawar farashin kayayyaki.”

Shugaba Buhari ya ce ya samu labarin cewa tun lokacin da aka fara aiwatar da amfani da sabbin kudaden, an samu nasarar maido da kusan Naira tiriliyan 2.1 zuwa cikin bankuna wanda a baya suke a hannun jama’a  adadin kaso 80 ke nan.

Ta fuskar sha’anin tsaro kowa, shugaba Buhari ya ce sauyin kudaden zai baiwa jami’an tsaro cikakkiyar damar yaki da ayyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce sakamakon jin ta bakin masu ruwa da tsaki da gwamnonin jahohi kan yanayin da ’yan kasa suke ciki, ya bada umarnin amfani da tsohuwar Naira dari 2 amma zuwa 10 ga watan Afirilu kawai, sai dai duk da haka sabuwar Naira dari 2 za ta ci gaba da wanzuwa a bankuna. (Garba Abdullahi Bagwai)