logo

HAUSA

Messi Mbappe da Benzema na takarar gwarzon dan kwallon kafar duniya na hukumar FIFA na 2022

2023-02-17 19:03:24 CMG Hausa

Taurarin kwallon kafa dake taka leda a manyan kulaflikan duniya 3, Lionel Messi, da Kylian Mbappe da Karim Benzema, su ne ke takarar zama gwarzon dan kwallon duniya na hukumar FIFA na shekarar 2022 ajin maza, kamar dai yadda hukumar ta FIFA ta samar da hakan.

A bangaren Messi, wanda shi ne kyaftin din kungiyar kasar Argentina da ta lashe kofin duniya na FIFA a bara a kasar Qatar, bayan doke Faransa a wasan karshe da ya yi matukar kayatarwa, dan wasan ya riga ya lashe kyautar kwallon zinari na gasar ta cin kofin duniya, yayin da takwaransa na Paris Saint-Germain Mbappe ya lashe kyautar takalmin zinari, bayan ya zura jimillar kwallaye 8 a raga a gasar ta Qatar.

Daya dan takarar da shi ma ke buga kwallo mai kayatarwa wato Benzema, shi ma ya lashe kyautar Ballon d'Or, bisa rawar da ya taka wajen lashe gasar UEFA Champions League, da La Liga tare da kungiyar Real Madrid, ko da yake bai halarci gasar Qatar ba, saboda jinya da yake fama da ita.

A ajin mata ma, ‘yar wasan Sifaniya Alexia Putellas, da ‘yar wasar Ingila Beth Mead, da Alex Morgan ta Amurka, su ne wadanda ke takarar lashe tauraruwar kwallo ta duniya.

Bisa tsarin ba da lambobin yabon, a ranar 27 ga watan Fabarairun nan ne za a mika wa wadanda suka yi nasara kyautukan su, ciki har da ‘yan wasa mafiya hazaka maza da mata, da kociya mafiya kwarewa maza da mata, da masu tsaron gida mafiya kwarewa maza da mata, da lambar yabo ta “Puskas” wadda ake baiwa kwallo da aka ci mafi kayatarwa ta 2022. Za a gudanar da bikin mika lambobin yabon ne a birnin Faris na Faransa.


Tsohon kocin Croatia Blazevic ya rasu

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafar Croatia Miroslav Ciro Blazevic ya rasu, bayan ya sha fama da cutar daji, ya kuma rasu ne kwanaki 2 kacal kafin cikar sa shekaru 88 a duniya.

An haifi Blazevic ne a garin Travnik na Bosnia Herzegovina a shekarar 1935, ya kuma fara horas da kungiyoyin kwallon kafa a shekarun 1960 a Switzerland. Kuma cikin shekaru 40, ya jagoranci kungiyoyin kasashen Switzerland, da Croatia, da Iran, da Bosnia Herzegovina, da tawagar Sin ta ‘yan kasa da shekara 23, da kuma kulaflikan Dinamo Zagreb, da Grasshopper Zurich da Shanghai Shenhua.

A shekarar 1998, yayin da yake horas da kungiyar kasar Croatia, Blazevic ya yi nasarar lashe tagulla a gasar cin kofin duniya na Faransa. A Croatia, ana kiran sa da babban mai horas da masu horaswa, yana kuma da matukar farin jini tsakanin ‘yan wasa da masu horaswa, da ma sauran al’ummar kasar, wadanda har kullum yake nunawa kauna.

Dubban ‘yan Croatia sun ziyarci gawarsa domin karramawa ga kwararren kocin, ciki har da firaministan Croatia Andrej Plenkovic. Da yake tsokaci game da mutuwar shahararren kocin ta wani sakon tiwita, Plenkovic ya ce "Ciro, wanda ya lashe lambar tagulla a gasar cin kofin duniya na 1998, za a dade ana tuna shi a kundin tarihin al’ummar Croatia, da fannin wasannin kasar. Ilimin sa, da nasarorin sa, da tallafawa al’umma zai ci gaba da zama abu mai karfafa gwiwa ga jagororin gobe".

Shi ma babban manajan kungiyar kwallon kafar Croatia Zlatko Dalic, ya ce Blazevic ne ubangidan sa a fannin kwallo, kuma muhimmin jigo da ya karfafa masa gwiwar kaiwa inda yake a yanzu, da duk nasarorin da ya cimma a matsayin koci. Dalic ya ce "Har abada zan ci gaba da gode masa, da yi masa addu’a, tare da sadaukar da hidimata gare shi da iyalan sa".


A watan Janairu FIFA ta tabbatar da farfado da kasuwar musayar ‘yan kwallo

Takardun hotuna da hukumar FIFA ta fitar a ranar Alhamis, sun tabbatar da dawowar hada hadar kasuwar musayar ‘yan kwallo, tun daga watan Janairun bana.

A watan Janairun bana, adadin musayar ‘yan kwallo ajin maza ta kasa da kasa ta kai 4,387, adadin da ya kai sabon matsayin koli a watan, tun bayan kaddamar da sabon tsarin musayar ‘yan kwallo a shekarar 2010.

Shekaru 3 ke nan a jere, hukumar FIFA tana wallafa irin wadannan bayanai bayan kammala musayar ‘yan kwallo ta kasa da kasa a watan Janairu, kuma yanzu haka a karo na gaba, za a sake bude wannan dama ne a watan Satumba, bayan kammalar wa’adin tsakiyar shekara na rajistar ‘yan wasa.

A cewar rahoton, adadin kudaden da kulaflika suka kashe a watan Janairu ya karu, zuwa dalar Amurka biliyan 1.57, adadin da ya karu da kimanin kaso 17 bisa dari, idan an kwatanta da adadin na shekarar 2018.

Kulaflikan Ingila ne ke kan gaba, wajen kashe kudade, da yawan kudi har kimanin dala miliyan 898.6, adadin da ya kai kaso kusan 57.3 bisa dari, cikin jimillar kudaden da aka kashe a lokacin.

Hukumar FIFA ta sanar da cewa, ajin mata na musayar ‘yan wasan kwallon kafa ma, ya samu karuwa mafi girma, inda aka yi musaya har 341.


‘Yan tseren Afirka sun lashe gasar tseren yada kanin wani ta Hong Kong

Kimanin ‘yan tsere 37,000 ne suka kammala gudu a gasar yada kanin wani ta yankin Hong Kong karo na 25, wadda aka gudanar a ranar Lahadi, gasar da ‘yan tsere daga nahiyar Afirka suka lashe mafi yawan kyaututtukan ta.

Gasar wadda ke gudana duk shekara, tana kunshe da gudun rabin zango da gudun kilomita 10, kuma a wannan karo, an kaddamar da ita ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, kuma masu nazarin ta sun ce yanayin dumi sosai, ya karawa masu tseren wahala yayin da suke gudu.

Dan wasan tsere Philimon Kiptoo Kipchumba daga Kenya, shi ne ya lashe gasar ajin maza cikin sa’o’i 2 da mintuna 10 da dakika 47, sai kuma dan tseren kasar Habasha da ya zo na biyu.

A bangaren mata kuwa, ‘yan tseren kasar Habasha 3 ne suka lashe lambobin yabo na ukun farko, kuma Fantu Eticha Jimma ce kan gaba a matsayin farko, inda ta kammala tseren ta cikin sa’o’i 2 da mintuna 27 da dakika 50.


LeBron James ya karya matsayin bajimta a gasar NBA

Dan wasan kwallon kwando dake bugawa kungiyar Los Angeles Lakers wasa LeBron James, ya karya matsayin bajimtar da aka kafa a gasar da hukumar NBA ke shiryawa, inda a yanzu ya wuce tarihin da Kareem Abdul-Jabbar ya kafa na tsawon shekaru kusan 39. Yayin da ya bugawa Lakers din wasannin kaka 14, Abdul-Jabbar, wanda sau 6 yana lashe kambin MVP na hukumar ta NBA, ya ci maki 38,387 cikin shekaru 20 na buga wasan sa.

A nasa bangare, LeBron James ya kafa sabon tarihi ne a wasan da kungiyar sa ta buga da takwararta ta Oklahoma City Thunder a daren ranar Talata. Kafin wasan, James na bukatar maki 36 kafin karya matsayin bajimtar da aka kafa a baya a gasar NBA. Yayin da ya rage dakika 10.9 ta wasan kwata ta 3, da aka buga a filin wasa na Los Angeles' Crypto.com, James ya samu maki 2 na karshe da yake bukata. Nan take kuma jami’an hukumar NBA suka tsayar da wasan da ake bugawa har tsawon ‘yan mintoci, domin karrama kwazo James.

Abdul-Jabbar na cikin wadanda suka halarci wasan, ya kuma ganewa idanun sa nasarar da James ya cimma, inda filin wasan ya cika da Shewa da murnar wannan nasara ta James.

Sai dai kuma duk da wannan nasara, da tarihi da James ya kafa a wasan, Lakers ta yi rashin nasara a hannun abokiyar wasan ta da ci 133 da 130.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Kwamishina a hukumar ta NBA Adam Silver, ya ce “Muna jinjinawa LeBron, bisa kafa wannan tarihi a wasa mai tarin mabiya, inda a yanzu ya zamo ja-gaba a jerin ‘yan wasan dake buga gasar NBA mafiya zura kwallo a raga. Wannan babbar nasara ce mai tabbatar da kasancewar sa zakara, a wannan fage cikin shekaru sama da 20 da ya shafe yana buga wannan gasa. Kuma abun ban sha’awa ne, ganin yadda LeBron ke ci gaba da wasa a ajin kwararru, kuma har yanzu bai kammala cimma nasarori a fagen ba”.