logo

HAUSA

Hanyar da Sin take bin wajen raya kasar dogaro da aikin gona za ta baiwa duk fadin duniya kwarin gwiwa

2023-02-17 09:45:15 CMG HAUSA

DAGA MINA

Abokai, na taba fada muku cewa, gari na lardin Hunan ne, wurin da masanan aikin gona karkashin jagorancin Yuan Longping, wanda aka yi masa lakabi da “Mahaifin samar da irin shimkafa mai aure” na Sin, sun fara nazarin renon sabon irin shimkafa ta hanyar aure karo na farko. Bayan kokarin da suka yi a cikin daddaden lokaci, an kirkiro irin shimkafa ta hanyar aure, abin da ya magance matsalar karancin abinci a nan kasar Sin.

Baya ga wannan kuma, kwanan baya, kwamitin kolin jam’iyyar JKS, ya gabatar da kundin koli na farko na shekarar 2023, inda a karon farko aka gabatar da ra’ayin inganta karfin kasar Sin ta hanyar raya aikin gona.

Bunkasuwar al’umma na dogaro da isashen hatsi, abu ne da ya zama tushen bunkasuwar kasar. Kaza lika Sin ba za ta samun bunkasuwar a zo a gani ba, idan aka bar sha’anin noma cikin halin koma baya.

Marigayin shehun malam Yuan Longping, ya taba fadawa manema labarai cewa, yana da burika biyu. Na daya irin da ya kirkiro a sabon mataki ya yi armashi matuka. Na biyu kuma, nazarin da tawagar sa take yi ya taimakawa al’ummar duniya baki daya.

Kimiyar renon iri ta hanyar aure da tawagar sa ta kirkiro, ta fita zuwa kasashe da yankuna fiye da 60 ciki hadda Amurka. Alal misali, a Najeriya, yawan hatsin da aka girba daga irin da aka shigar daga Sin ya karu da kashi 25% bisa na baya a gonan gwaji. Matakin da ya bayyana cewa, hanyar da Sin take bi wajen inganta karfin kasar, wajen dogaro da aikin gona, ba ma kawai zai amfani kasar Sin ba ne, har ma zai samar da taimakon kimiyya a fannin aikin gona don samar da isashen hatsi a duniya.

Mu Bil Adama, muna da kyakkyawar makoma ta bai daya ne, kuma bunkasuwar Sin za ta taka rawar gani ga bunkasuwar duniya baki daya, kuma Sin za ta kara hadin kai da kasashe daban-daban, bisa ra’ayin hakuri da juna, da kawo moriyar juna don samun bunkasuwa tare. (Mai zana da rubuta: MINA)