logo

HAUSA

Sin: Kudurin Da Majalisar Wakilan Amurka Ta Yanke Game Da Balan-balan Din Sin Kutungwilar Siyasa Ne

2023-02-16 19:41:31 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce a ‘yan kwanakin nan, majalissar wakilan Amurka, ta zartas da wani kuduri game da balan-balan maras matuki na kasar Sin, wadda bisa kuskure ta shiga samaniyar Amurka. Kuma kudurin ya yi watsi da ainihin gaskiyar abun da ya faru, kuma babu komai a cikin sa illa kutungwilar siyasa.

Da yake bayyana hakan a yau Alhamis, Wang Wenbin ya ce kasar Sin na kira da babbar murya ga majalissar dokokin Amurka, da ta martaba gaskiya, da kimar dokokin kasa da kasa, da kuma ginshikan dake jagorantar cudanyar kasashen duniya, ta kuma gaggauta dakatar da shafawa kasar Sin bakin fenti, da nacewa matakan da ka iya rura wutar sabani.  (Saminu Alhassan)