logo

HAUSA

Najeriya ta bude cibiyar tuntuba ta gaggawa domin dakile satar mutane da ayyukan ta’addanci

2023-02-16 15:46:04 CMG Hausa

Jaridar “The Guardian” da ake wallafawa a Najeriya, ta hakaito karamin minista mai kula da kasafin kudi da shirin raya kasa na kasar Mr. Clem Agba, na cewa rundunar tsaro da kare fararen hula ta Najeriya, ta kafa cibiyar tsaron makarantu, da tuntuba ta gaggawa, don kara karfin kula, da kuma kare daliban makarantun kasar.

Ministan ya ce gwamnatin tarayyar Nijeriya, za ta samar da kudade ga shirin tsaron makarantu a kan lokaci, ta yadda za a iya tabbatar da ganin yara ’yan makaranta sun samu ilimi a makarantunsu lami lafiya, ba tare da damuwar rashin tsaro, ko sace su domin neman kudin fansa ba. (Safiyah Ma)