logo

HAUSA

Xi ya aike da sakon murnar bude taron hadin gwiwar zuba jari tsakanin Sin da kasashen tsakiyar Asiya 5

2023-02-16 13:51:57 CMG Hausa

A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon murnar bude taron dandalin tattauna hadin gwiwar masana’antu, da zuba jari tsakanin kasar Sin da kasashe 5 dake tsakiyar Asiya, wadanda suka hada Kazakhstan, Uzbekistan, Tajikistan, Kyrgyzstan da Turkmenistan.

A cikin sakonsa, Xi ya yi nuni da cewa, tun bayan da kasar Sin ta daddale huldar diplomasiya da wadannan kasashe biyar shekaru 30 da suka gabata, sassan sun kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare bi da bi, domin samun ci gaba tare, ta hanyar gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu. Kana sun kasance abin koyi wajen kafa sabuwar huldar kasa da kasa ga sauran kasashen duniya. Ya ce yanzu haka, kasar Sin da kasashen biyar, suna kokarin zurfafa hadin gwiwa kan masana’antu da zuba jari, lamarin da zai ingiza ci gaba, da wadata a yankin.

Har ila yau, kasar Sin tana son more babbar kasuwarta, da cikakken tsarin sana’o’i, da fasahohin zamani da kasashen dake tsakiyar Asiya, ta yadda za su yi kokari tare, domin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci a yankin, tare kuma da gina kyakkyawar makomar Sin da tsakiyar Asiya ta bai daya.

Hukumar kwaskwarima da raya kasa ta kasar Sin, da gwamnatin lardin Shandong na kasar ne suka kaddamar da taron dandalin, bisa taken “Samun moriya da ci gaba tare, da kuma ingiza ci gaban tattalin arziki mai inganci a yankin”, a yau a birnin Qingdao na lardin Shandong. (Jamila)