Li Keqiang Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Sabon Firaministan Equatorial Guinea
2023-02-16 19:52:04 CMG Hausa
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya aikewa takwaransa na Equatorial Guinea Manuela Roka Botey, sakon taya murnar kama aiki a ranar 13 ga watan nan.
Cikin sakon na sa, Li Keqiang ya ce Sin da Equatorial Guinea, na morewa kawancen gargajiya, da amincewa juna ta fuskar siyasa, suna kuma morar hadin gwiwar su a fannoni masu tarin yawa.
Ya ce Sin na dora muhimmancin gaske, kan bunkasa hadin kan ta da Equatorial Guinea, kuma a shirya take ta yi aiki da kasar, wajen daga matsayin cikakken hadin gwiwa, da kawancen dake tsakanin sassan biyu zuwa wani sabon matsayi. (Saminu Alhassan)