Kwarin gwiwa game da kundin koli na farko
2023-02-16 09:05:51 CMG Hausa
A ranar Litinin 13 ga watan nan ne kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya fitar da kundin koli na farko na shekarar 2023. Kuma wannan ne karo na 20 a jere, cikin karnin nan na 21, da kwamitin kolin ke fitar da irin wannan kundin koli, domin bunkasa “aikin gona da yankunan karkara da kuma manoma”, wanda ya shafi sassa 9, wato tabbatar da ganin an samar da isasshen amfanin gona mai muhimmanci cikin gaggawa, da karfafa samar da manyan ababen more rayuwa na aikin gona, da kara nuna goyon baya a fannin kimiyya da fasaha, da kuma kayayyakin aikin gona.
Sauran su ne inganta sakamakon da aka samu a fannin kawar da kangin talauci, da inganta ci gaban masana’antun da ake bunkasa a yankunan karkara, da kuma taimakawa manoma da hanyoyin samun karin kudin shiga, sannan, da kokarin gina ni’imtattun kauyuka inda kowa zai so yin rayuwa, da aiki. Kaza lika akwai kyautata tsarin mulkin kauyuka dake karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta Sin, da kuma kara tabbatar da ganin an gudanar da manufofi, da yin kirkire-kirkire a kan tsari. (Safiyah Ma)