logo

HAUSA

An yi kira da a gaggauta dunkulewar Afirka a taron majalisar zartaswar AU

2023-02-16 13:47:46 CMG Hausa

A jiya Laraba ne aka kaddamar da taro karo na 42, na majalisar zartaswa ta kungiyar tarayyar Afirka AU a birnin Adis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, hedkwatar kungiyar, inda yayin taron na yini biyu, aka yi kira da a gaggauta dinke nahiyar Afirka, domin cimma burin raya nahiyar.

Yayin bikin bude taron da aka shirya, shugaban hukumar AU Mussa Faki Mahamat, ya yi tsokaci da cewa, bisa sakamakon da aka samu a fannin aiwatar da shirin shekaru goma na farko, na ajandar AU nan da shekarar 2063, wato tsakanin shekarar 2014 zuwa ta 2023, an lura cewa, kasashen Afirka sun samu babban ci gaba, a fannonin samun bunkasuwa mai dorewa, da karuwar tattalin arziki, amma duk da haka, akwai bukatar a ci gaba da yin kokari domin samun sabon ci gaba.

Mahamat ya kara da yin kira, da a ingiza zamanintar da masana’antu a nahiyar, tare kuma da gaggauta gina yankunan cinikayya marasa shinge a Afirka.

A nasa bangare kuwa, mukaddashin sakataren zartaswa na hukumar kula da tattalin arzikin kasashen Afirka ta MDD, Antonio Pedro, cewa ya yi gina yankunan cinikayya marasa shinge, zai ciyar da cinikayya dake tsakanin kasashen Afirka gaba, ta yadda kasashen za su samar da yawancin magunguna, da abinci, da takin zamanin da suke bukata da kansu. A sa’i daya kuma, yarjejeniyoyin cinikayyar maras shinge da aka daddale tsakanin kasashen nahiyar Afirka, za su samar da karin damammakin aikin yi ga mata da matasa, wanda hakan zai rage rashin daidaito, da talauci, tare kuma da kyautata muhallin zaman takewar al’umma a nahiyar ta Afirka. (Jamila)